Isa ga babban shafi

Jiga-jigan tsohuwar gwamnatin Sudan sun tsere daga gidan Yari

Wasu jiga-jigai a tsohuwar gwamnatin Sudan da aka hambarar a shekarar 2019 sun tsere daga gidan yarin da ake tsare da su a babban birnin kasar Khartoum, cikin su har da wani wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo, lamarin da ya sa ake fargabar wargajewar kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta da  aka cimma a rikicin da ake yi a kasar. 

Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Khartoum babban birnin kasar Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Tserewar kusoshin na rusashiyar gwamnatin Omar Al-Bashir, har da Harun Ahmed wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan keta haddin bil adama ya haddasa fargabar rincabewar fadan da ake gwabzawa a Sudan. 

Ahmed Haroun da kansa ya tabbbatar da cewa da shi sauran abokansa sun arce daga gidan yarin Kober a daren Talata, inda a wani sakon bidiyo ya ce kada a damu da batun tsaron lafiyarsu saboda sun isa su samar wa kansu da tsaro. 

Wata sanarwa da sojin Sudan ta fitar ta ce ta dauki wasu jami’an tsohuwar gwamnatin kasar  ciki har da jagoransu da kansa Omar Al- Bashir  mai shekaru 79 zuwa wani asibitin soji sakamakon yanayi na tabarbarewar lafiya da suke ciki. 

Wannan ne karo na 3 da wasu  fursunoni ke tserewa daga gidan yari ta wajen amfani da kafar da wannan yaki da ake tsakanin dakarun da ke biyayya da jagoran mulkin soji Abdel Fattah al-Burhan da kuma rundunar kai daukin gaggawa a karkashin jagorancin mataimakinsa,  Mohammed Hamdan Daglo. 

Rikicin da ya barke kusan makwanni 2 da suka wuce yayi sanadin mutuwa kusan mutane dari 500 tare da jikatta sama da dubu 4000. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.