Isa ga babban shafi
Sudan-ICC

ICC za ta fara sauraron shari'ar zargin aikata laifukan yaki a Sudan

Yau talata kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC za ta fara sauraron shari’a kan zargin aikata laifukan yaki a Sudan shekaru 20 bayan rikicin kasar da ya hallaka dubunnan fararen hula.

Ginin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague a Netherlands.
Ginin kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague a Netherlands. REUTERS/Jerry Lampen/File Photo
Talla

Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman da ke matsayin tsohon jagoran mayakan sa kai na kungiyar Janjaweed na fuskantar tuhume tuhume guda 31  ciki har da laifukan yaki da na cin zarafin bil’adama da ya kunshi kisan kai fyade da azabtarwa baya ga tantagaryar tsangwama ga tsiraru.

Lauyan kare hakkin dan adam na Sudan Moassad Mohamed Ali ya bayyana ranar faro wannan shari’a a matsayin mai cike da farin cikin ga dubunnan wadanda yakin ya shafa don tabbatar musu da adalci.

Masu shigar da kara na kotun ta ICC sun bayyana Abd-Al-Rahman wanda aka fi sani da Ali Kushyab a matsayin babban kwamandan Janjaweed da ya jagoranci dubunnan mayakan kungiyar tsakanin shekarun 2003 zuwa 2004 wajen aikata kashe-kashe mafi kololuwar muni a lokacin rikicin na Darfur.

Sai dai Abd-Al-Rahman ya musanta dukkanin zarge-zargen masu shigar da karar akansa inda a lokuta da dama shi da lauyoyin da ke kare su ke ci gaba da ikirarin cewa anyi kuskuren tuhumarsa da laifukan da wani daban ya aikata.

A cewar lauyoyin tsohon jagoran na Janjaweed umarnin da ya bayar a wancan lokaci bashi da masaniyar zai kai ga aikata laifukan yaki.

A watan Yunin 2020 ne Abd-Al-Rahman ya mika kansa ga kotun da ke da Shalkwata a birnin Hague shekaru 13 bayan shelanta nemansa kan zargin aikata laifukan yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.