Isa ga babban shafi
Libya-ICC

ICC na neman dan Ghaddafi ruwa a jallo

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa na neman dan tsohon shugaban Libya Moamer Ghaddafi, wato Seif al-Islam, ruwa a jallo, wanda tuni ya yi rajistar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na watan Disamba.

Saif al-Islam, da ga marigayi shugaban Libya Moammar Ghaddafi.
Saif al-Islam, da ga marigayi shugaban Libya Moammar Ghaddafi. AFP/ Mahmud Turkia
Talla

Shekaru da dama ana neman cikakken bayani game da inda mutumin da aka dade ana yin la'akari da shi a matsayin wanda zai gaji tsohon shugaban na Libya,  wanda aka kashe a wata zanga-zangar da jama'a suka yi a shekara ta 2011.

Bayyanar Seif al-Islam na farko a bainar jama'a cikin shekaru ya zo ne ta hanyar wata hira da jaridar New York Times da aka wallafa a watan Yuli, ko da yake a lokacin bai bayyana cewa zai shiga siyasar kasar ba.

A ranar Lahadi, hukumar zaben kasar Libya ta bayyana cewa, Seif al-Islam ya yi rajistar tsayawa takara a babban zaben da ake shirin gudanarwa ranar 24 ga watan Disambar 2021, a kasar mai arzikin man fetur a arewacin Afirka.

Rahotanni sun ruwaito cewa, an gano shi yana rajistar takararsa sanye da tufafin gargajiya.

 

wanda aka haifa a shekara ta 1972, Seif al-Islam, wanda sunansa ke nufin "takobin Musulunci", shi ne na biyu a cikin 'ya'yan tsohon shugaba Ghaddafi su takwas, wanda ya kasance babban dan matarsa ta biyu Safiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.