Isa ga babban shafi

Yarjejeniyar tsagaita wutar Sudan mai rauni ta shiga yinin karshe

Rahotanni daga Sudan, sun ce an dan samu raguwar kazamin fadan da ake gwabzawa tsakanin rundunonin dakarun da ke rikici da juna, sai dai an cigaba da  musayar wuta a wasu birane, musamman a Khartoum, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wutar kwanaki ukun da ke shirin karewa a yau.

Wani yankin Khartoum babban birnin Sudan. 25 ga Afrilu, 2023.
Wani yankin Khartoum babban birnin Sudan. 25 ga Afrilu, 2023. © Marwan Ali / AP
Talla

A ranar Laraba, rana ta biyu bayan tsagaita bude wutar, wasu shaidun gani da ido sun ce an kai hare-hare ta sama a jihar East Nile da ke gabas da birnin Khartoum, yayin da kuma aka jiyo karar fashewar bam a kusa da wani sansanin dakarun rundunar musamman ta RSF da ke fafatawa da sojojin Sudan.

A arewacin birnin Khartoum kuwa, jiragen yaki ne suka rika shawagi a wasu yankuna, yayin da dakarun da ake kyautata zaton na RSF ne daga kasa, suka rika kokarin kakkabo su da manyan bindigogi.

Tuni dai rundunar sojin Sudan da ke karkashin shugaba Abdul Fattah Al Burhan ta ce za ta aika da wakili zuwa Juba, babban birnin makwafciyarta Sudan ta Kudu, domin tattaunawa da dakarun RSF, a karkashin shiga tsakanin kungiyar hadin kasashen gabashin Afirka ta IGAD, domin tattaunawa kan bukatar tsawaita wa’adin yerjejeniyar tsagaita bude wuta da karin sa'o'i 72, la’akari da cewar da yammacin wannan alhamis wadda ke aiki za ta kare.

A ci gaba da kwashe fararen hula baki da ‘yan kasa daga Sudan kuwa, sama da mutane 1,600 daga kasashe akalla 50 ne suka isa Saudiyya ta ruwa a ranar Laraba, yayin da Birtaniya ta samu nasarar kwashe na ta ‘yan kasar zuwa, Cyprus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.