Isa ga babban shafi

Bangarorin Sudan ba su da niyyar kawo karshen rikicin nan kusa - MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace, babu wata alama da ke tabbatar da cewa bangarorin da ke rikici da juna a Sudan da gaske suke don kawo karshen fadan da ake gwabzawa, duk da yarjejeniyar tsagaita wuta na sa’o’i 72 da aka cimma, an ci gaba da bude wuta a wasu wurare.

Janar - janar din Sudan biyu dake fada da juna Abdel Fattah al-Burhan da kuma Mohamed Hamdan Daglo Hemedti.
Janar - janar din Sudan biyu dake fada da juna Abdel Fattah al-Burhan da kuma Mohamed Hamdan Daglo Hemedti. © AFP
Talla

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Volker Perthes ne ya shaidawa taron kwamitin sulhu na Majalisar a birnin New York hakan ranar Talata, cewa bangarorin biyu da ke rikici da juna kowa ya yi imanin cewa yana daf da samun nasara.

Yana magana ne ta hoton bidiyo daga Port Sudan da ke gabashin kasar, inda Majalisar Dinkin Duniya da wasu suka kwashe wasu daga cikin ma'aikatansu zuwa can.

Tasirin yarjejeniyar tsagaita wuta

Jami’in yace yarjejeniyar tsagaita wuta na sa’o’i 72 da aka cimma sakanin bangarorin biyu ya dan kawo sa’ida, amma an samu rahotannin artabu a wurare masu muhimmanci na kasar ciki harda babban birnin Khartoum da wasu yankuna, yayin aka ci gaba da jibge sojoji da kayan aiki a wasu wurare.

Birnin Khartoum ya koma fagen daga inda ake kaiwa juna hare-hare da manyan bindigogi da tankokin yaki, da kuma hari ta sama, lamarin da ya yi sanadin kashe akalla mutane 459, yayin da sama da 4,000 suka jikkata, tare da katsewar wutar lantarki da ruwa da takaita rabon abinci a kasar da kashi uku na al’ummarta miliyan 46 ke dogaro da taimakon abinci.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana tashin hankalin na Sudan a matsayin abin takaici, inda ya gargadi taron Majalisar a ranar Talata cewa yakin na iya yaduwa zuwa wasu kasashen yankin.

Baki sun isa Saudiya

A halin da ake ciki  wani jirgin ruwa dauke da fararen hula 1,687 daga kasashe fiye da 50 da suka tsere daga rikicin Sudan ya isa kasar Saudiyya, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana, wanda shi ne aikin ceto mafi girma da masarautar Gulf ta yi a halin yanzu.

Sanarwar ta ce, kawo yanzu an kwashe mutane 2,148 zuwa masarautar daga Sudan, ciki har da baki fiye da 2,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.