Isa ga babban shafi

An tsagaita wuta na sa'o'i 72 a rikicin Sudan - Amurka

Amurka ta ce bangarorin Sojin Sudan biyu da suka haddasa rikicin da ya salwantar da dumbin rayuwa tare da tilastawa baki barin kasar, sun amince da tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 72.

Wasu gine-gine da suka fuskanci hare-hare a birinin Khartoum na Sudan. 23/04/23
Wasu gine-gine da suka fuskanci hare-hare a birinin Khartoum na Sudan. 23/04/23 AFP - HANDOUT
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ne ya bayyana wannan ci gaban da aka samu a litinin din nan, bayan da aka shafe kwanaki 10 ana gwabza kazamanin fada a biranen Sudan, inda aka kashe daruruwan mutane tare da raunata dubbai, yayin da aka shiga kwanakin na uku na kokarin fitar da baki daga kasar.

Tsagaita wuta

Yunkurin kawo karshen rikicin da aka yi a baya dai ya ci tura, to sai babban jami’in diflomasiyyar Amurkan yace bangarorin dakarun gwamnati karkashin Aldel Fattah al-Burhan da na tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo sun amince da tsagaita wutar kwanaki uku da ya fara aiki tun cikin daren litinin bayan shiga tsakani na kwanaki biyu, inji Antony Blinken.

Sanarwar Blinken na zuwa ne sa'o'i biyu gabanin tsagaita wutar ta soma aiki, daidai lokacin da Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa kasar Sudan ta sunduma wani bala'i da bata taba gani ba, biyo bayan fadan da ake gwabzawa a babban birnin kasar, Khartoum, da ma wasu manyan birane.

Sama da mutane 427 suka mutu

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla mutane 427 ne suka mutu sannan fiye da 3,700 suka jikkata, kuma yanzu haka mutane da dama na fama da matsanancin karancin ruwa da abinci da magunguna da kuma matsalar rashin wutar lantarki da intanet.

Fiye da mutane 4,000 ne suka tsere daga kasar a wani shirin kwashe baki ‘yan kasashen waje da aka fara a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.