Isa ga babban shafi

Kasar Canada ta katse huldar diflomasiyya da Sudan saboda rikici

Kasar Canada ta sanar a yau Lahadi da cewa ta dakatar da ayyukan diflomasiyya na wani dan lokaci a Sudan, tana mai cewa ma'aikatanta za su yi aiki daga "wuri mai aminci a wajen kasar", yayin da ake gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da Dakarun RSF.

Dakarun gwamnatin Sudan
Dakarun gwamnatin Sudan AFP - ABUBAKARR JALLOH
Talla

Sanarwar da hukumomin Canada suka fitar, halin da ake ciki a Sudan ya tabarbare cikin hanzari, wanda hakan ya sa ba za a iya tabbatar da tsaron lafiyar jami'anmu a Khartoum ba.

"Jami'an diflomasiyyarmu suna cikin koshin lafiya kuma suna aiki daga wajen kasar," in ji ministar harkokin wajen kasar Canada Mélanie Joly a shafin Twitter ba tare da bayar da karin bayani ba.

A jiya Asabar da ta gabata ne Saudiyya ta sanar da cewa 'yan kasar Canada na daga cikin mutane sama da 150 da suka hada da jami'an diflomasiyya da jami'an kasashen waje da aka kwashe daga Sudan a wani samame da sojojin ruwan kasar suka jagoranta.

Ma'aikatan da aka dauka a cikin gida suna ci gaba da zama a babban birnin Sudan, in ji hukumomin Canada, suna mai jaddada cewa suna nazarin "dukkan zabin da za a yi don tallafa musu bisa la'akari da yanayin da ke faruwa a kasar ta Sudani".

Tawagar jami'an diflimasiyya na ficewa daga kasar Sudan
Tawagar jami'an diflimasiyya na ficewa daga kasar Sudan AFP - ABUBAKARR JALLOH

Wannan sanarwa daga Canada na zuwa ne a daidai lokacin da Jamus da Birtaniya da sauran kasashe suka sanar da kwashe 'yan kasarsu ko jami'an diflomasiyyarsu.

Shugaban Amurka Joe Biden ya kuma sanar da cewa sojojin sun gudanar da wani samame na zakulo ma'aikatan gwamnatin Amurka daga birnin Khartoum.

Birnin Khartoum
Birnin Khartoum © AFP

Sudan ta shiga mako na biyu ana gwabza kazamin fada. Rikicin dai yana adawa da sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhane, wanda ke mulkin Sudan tun daga shekarar 2021, da kuma tsohon mataimakinsa wanda ya zama abokin hammaya, Janar Mohamed Hamdane Daglo, wanda ke ba da umarnin Rapid Support Forces.

Har yanzu adadin wadanda suka mutu na wucin gadi ya kai sama da 420 da suka mutu yayin da 3,700 suka jikkata, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.