Isa ga babban shafi

Kura ta lafa a Sudan bayan kusan mako guda na kazamin rikici

Rahotanni daga Sudan na cewa an samu saukin rikicin da ake ta gwbazawa a cikin ungwannin birnin Khartoum a Juma’ar nan, bayan kiraye kirayen tsagaita da aka yi ta yi don samun sukunin gudanar da bikin Salla karama ta karshen watan Ramadan.

Akasarin unguwannin birnin Khartoum babu kowa sakamaakon rikicin.
Akasarin unguwannin birnin Khartoum babu kowa sakamaakon rikicin. AP - Marwan Ali
Talla

Sama da mutane 400 ne aka ruwaito sun mutu, kana dubbai suka jikkata tun da wannan rikici ya barke a ranar Asabar tsakanin rundunar sojin kasar a karkashin shugaba Abdel Fattah al-Burhan da runduna ta musamman, wanda mataimakinsa  Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta.

A ranar Juma’a rundunar sojin kasar ta sanar da cewa ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki  3 don bai wa al’ummmar kasar damar gudanar da bikin sallah karama, tare da barin kayayyakin agajji su shiga yankunan da ake da bukatar su.

Shaidu daga yankuna da daman a birnin Khartoum sun ce  kura ta  lafa a yammacin Juma’a, bayan luguden wuta da aka kwashe kwanaki kusan 7 ana yi a birnin.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce dakarun sojin kasar na fatan 'yan tawayen za su bi dukkan sharuddan tsagaita bude wuta da kuma dakatar da duk wani yunkuri na soji da zai kawo mata cikas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.