Isa ga babban shafi

Sudan: Dakarun RSF sun sanar da tsagaita wutar sa'o'i 72

Dakarun musamman na RSF da ke gwabza fada da sojojin Sudan, sun amince da tsagaita bude wuta tsawon sa'o'i 72, domin bayar da damar gudanar da ayyukan jin kai, matakin da suka ce zai fara aiki daga karfe shida na safe agogon kasar a yau Juma’a.

Wasu tankokin yaki da aka ragargaza a kudancin Khartoum babban birnin kasar Sudan. 20 ga Afrilu, 2023.
Wasu tankokin yaki da aka ragargaza a kudancin Khartoum babban birnin kasar Sudan. 20 ga Afrilu, 2023. AP - Marwan Ali
Talla

Sai dai ya zuwa wannan lokacin nan babu wani karin haske kan ko rundunar sojojin gwamnati ta amince da yarjejenniyar tsagaita wutar, kasancewar shugaba Janar Abdel Fattah Al Burhan, bai ambaci tsagaita bude wutar ba a wani jawabinsa da aka watsa ta shafin Facebook.

Tun a ranar Alhamis ne dai kasashe da dama gami da Majalisar Dinkin Duniya ke kira da a tsagaita wuta a kasar ta Sudan domin bayar da damar fara tattaunawar Sulhu.

Alkaluman da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya ta fitar, sun nuna cewar mutane tsakanin dubu 10 zuwa dubu 20 sun tsere daga Sudan zuwa kasar Chadi domin samun mafaka daga tashin hankalin da ake yi.

Hukumar ta ce mafi rinjayen adadin mutanen da suka tsere daga Sudan din sun fito ne daga yankin Darfur.

A ranar Alhamis ministan tsaron Chadi Janar Daoud Yaya Ibrahim ya sanar da cewar akalla sojojin Sudan 320 suka gudu zuwa cikin kasar ta su domin samun mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.