Isa ga babban shafi

Sama da fararen hula 270 aka kashe a rikicin Sudan

Ofisoshin Diflomasiyar kasashen ketare 14 a Sudan sun ce adadin fararen hular da aka kashe a fafatawar da ake ci gaba da yi tsakanin magoya bayan shugaban mulkin sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da magoya bayan mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo sun kai akalla 270. 

Wani mutum kenan, da ke duba irin barnar da aka gidansa, yayin gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun kai daukin gaggawa na musamman a Sudan.
Wani mutum kenan, da ke duba irin barnar da aka gidansa, yayin gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun kai daukin gaggawa na musamman a Sudan. © REUTERS
Talla

Wata sanarwar da ofishin jakadancin Amurka ya gabatar a madadin ofisoshin kasashen ketare 14 a Khartoum tace adadin wadanda suka mutu daga bangaren fararen hula ya kai 270, yayin da wasu da dama suka jikkata, kuma suka kasa zuwa asibiti saboda kazancewar tashin hankalin. 

Rahotanni sun ce dubban fararen hula na ci gaba da tserewa daga bornin Khartoum domin samun mafaka, yayin da shaidun gani da ido ke cewa gawarwakin jama’a na zube na kasa, yayin da shirin tsagaita wutar da aka sanar jiya ta kasa dakatar da tashin hankalin. 

Bayanai sun ce jami’an diflomasiya dake Sudan basu tsira daga irin wadannan hare haren da ake samu daga bangarorin biyu ba, yayin da shugaban aikin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths yace sun samu rahotan hari da kuma zin zarafin ma’aikatan agaji mata. 

Rahotanni sun ce wannan tashin hankali ya biyo bayan kokawar mulki tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa da kuma kin aiwatar da Shirin sanya jami’na tsaro RSF cikin aikin soji kamar yadda bangarorin suka amince. 

Kungiyar likitocin kasar tace daga cikin asibitoci 59 dake birnin Khartoum, 39 sun daina aiki saboda tashin hankali wanda ya ritsa da mutane da dama. 

Japan tace tana Shirin kwashe ‘yan kasar kusan 60 dake Sudan, yayin da irin wannan yunkuri na Jamus wajen kwashe ‘yan kasar 150 a jiragen soji guda 3 ya kasa cimma biyan bukata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.