Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Sudan ya kai 134

Ambaliyar ruwa a kasar Sudan ta kashe akalla mutane 20 a cikin makon da ya gabata, kamar yadda hukumomin kasar suka sanar, lamarin da ya kara adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa tun da aka fara damina a watan Mayu zuwa 134.

Wata mata da ke kwashe kayan ta sakamakon ambaliya da ta rutsa da su
Wata mata da ke kwashe kayan ta sakamakon ambaliya da ta rutsa da su AP - Fareed Khan
Talla

Ofishin Birgediya Janar Abdul-Jalil Abdul-Rahim, shugaban kwamitin tsaron fararen hula na kasar Sudan, ya ce karin mutane 120 sun jikkata sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a makon da ya gabata.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin watan Agusta da farkon watan Satumba, ya shafe hanyoyi, gidaje, da muhimman ababen more rayuwa a fadin kasar, tare da katse hanyoyin samar da kayayyaki ga yankunan karkara dake bukatar agajin jin kai.

Bisa rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na baya-bayan nan da aka yi, ambaliyar ruwan ta shafi kimanin mutane 286,400, kana gidaje 16,900 suka lalace.

Hukumar ta ce a bana, mutane 74 ne suka nutse a ruwa, 32 kuma suka mutu a lokacin da gidajensu suka rufta, sai kuma wasu shida da suka mutu sakamakon wutar lantarki.

Kauyuka gabashi da yammacin kasar ne suka fi fama da mamakon ruwan sama a bana.

A ranar Laraba, kafar yada labaran kasar Sudan, SUNA, ta bayar da rahoton cewa, wata sabuwar masana'antar sukari da aka gina a kusa da birnin Kassala da ke gabashin kasar ta rushe sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A shekarar 2020, ambaliyar ruwa da ruwan sama mai karfi ya kashe mutane kusan 100 tare da lalata gidaje sama da 100,000 a kasar ta Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.