Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da jiyo amon fashe-fashe a Sudan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Karar fashewar gurneti ya girgiza babban birnin Sudan da yammacin ranar Talata duk da ikirarin tsagaita bude wuta a rana ta hudu da ake gwabzawa da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 200.

Yadda hayaki ya mamaye birnin Khartoum, na kasar Sudan, sakamakon hare-haren sama.
Yadda hayaki ya mamaye birnin Khartoum, na kasar Sudan, sakamakon hare-haren sama. AP - Abdullah Moneim
Talla

Cikin sanarwar da kowannensu ya fitar, sojojin Sudan da dakarun musamman na rundunar RSF sun zargi juna da rashin mutunta tsagaita bude wutar da aka cimma, abinda ya sa rundunar sojoji masu biyayya ga gwamnati shan alwashin ci gaba da kai hare-hare domin tabbatar da ikonsu a Khartoum da sauran yankuna. 

Rikicin da ya barke tsakanin babban hafsan sojin Sudan janar Abdul Fattah al Burhan da mataimakinsa Muhammad Hamdan Daglo kwanaki hudu da suka gabata, ya haifar da cikas ga shirin sake mika mulki ga farar hula, shekaru hudu bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir da ya fuskanci zanga-zangar gama gari da sojoji suka yi, wadanda kuma sake sake kawar da gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa karkashin Fira Minista Abdallah Hamdok shekaru biyu da suka gabata. 

Tun daga wannan lokacin, kasashen duniya ke ta kiraye-kirayen da a kawo karshen tashe-tashen hankula da suka haifar da karuwar rashin bin doka da oda da mutuwa asarar rayukan mutane da dama.

Kazamin fadan na Sudan da ya lakume rayukan mutane kusan 200, dai ya janyo abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin bala'in da ya kusan durkusar da tsarin kiwon lafiyar kasar. 

Shiga alamar sauti, dominn sauraron rahoton Bashir Ibrahim Idris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.