Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci gaggauta tsagaita wuta a Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gaggauta tsagaita wuta a kasar Sudan sakamakon tashin hankalin da aka samu wanda yayi sanadiyar kashe mutane sama da 180, yayin da daruruwa suka samu raunuka. 

Dakaru dauke da makamai a Sudan
Dakaru dauke da makamai a Sudan AFP - -
Talla

Sakatare Janar Antonio Guterres ya bayyana haka yayin jagorancin wani taron kwamitin sulhu na musamman domin tattauna rikicin na Sudan da zummar lalubo hanyoyin da za’a magance shi. 

Yayin gudanar da taron, Jakadan Majalisar na musamman a Sudan, Volker Perthes yayi jawabi ga wakilan kwamitin inda ya tabbatar da kazancewar rikicin wanda yace ya lakume rayukan mutane sama da 180 ya zuwa yammacin litinin din nan, yayin da wasu sama da 1,800 suka samu raunuka daban daban saboda amfani da manyan makaman da bangarorin dake rikicin biyu ke yi. 

Perthes yace ya zuwa wannan lokaci yana da wahala a bayyana yadda rikicin ke tafiya da kuma bangaren dake samun galaba, sai dai abin sani kawai shine yadda yake ritsawa da fararen hular da basu ji, basu gani ba. 

Fada ya barke a Sudan
Fada ya barke a Sudan AFP - -

Tashin hankalin na Sudan ya barke ne tun a ranar asabar da ta gabata, bayan an kwashe makwanni biyu ana cacar baka da kuma nuna yatsa tsakanin shugaban sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan dake samun goyan bayan sojoji da kuma mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo dake samun goyan bayan jami’an tsaro na musamman da ake kira RSF. 

Rahotanni sun ce anyi amfani da jiragen saman yaki da tankuna soji da kuma makaman atilare wajen kai munanan hare hare a unguwannin fararen hula dake Khartoum da wasu biranen kasar, abinda ya janyo kiran tsagaita wuta daga bangarori daban daban na kasashen duniya. 

Harabar filin tashi da saukar jirage a Sudan
Harabar filin tashi da saukar jirage a Sudan © INSTAGRAM @LOSTSHMI via REUTERS

Shugaban jami’an tsaro na musamman RSF kuma mataimakin al-Burhan, Daglo ya bukaci kasashen duniya da su shiga tsakani domin kawo karshen abinda ya kira rashin hankalin da al-Burhan ke yi wajen munanan hare hare akan fararen hula. 

Daglo yace zasu ci gaba da farautar sa wajen ganin sun gurfanar da shi a gaban shari’a. 

Hukumar Lafiya ta Duniya tace asibitoci da dama daga cikin guda 9 dake Khartoum na ci gaba da karbar tarin mutanen da suka jikkata sakamakon yakin, yayin da wasu mutane da dama suka makale a cikin gidajen su domin kaucewa rikicin. 

Rundunar sojin Sudan dake goyan bayan al-Burhan tace ita ke iko da birnin Omdurman, yayin da kafar talabijin din kasar da ya katse aikin sa ya dawo yana nuna sojojin suna sintiri, bayan yau da safe an samu barkewar wuta da tashin hayaki a birnin Khartoum. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.