Isa ga babban shafi

Mutane 56 sun mutu a rikici tsakanin dakarun Sudan

An ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun sojin Sudan da runduna ta musamman har zuwa sanyin safiyar Lahadin nan a babban birnin kasar Khartoum, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 56 tare da jikkata 170.

An ci gaba da gwabza fada har safiyar Lahadi a Sudan, a yayin da babu kowa a titunan babban birnin kasar, Khartoum.
An ci gaba da gwabza fada har safiyar Lahadi a Sudan, a yayin da babu kowa a titunan babban birnin kasar, Khartoum. © REUTERS / MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

A jiya Asabar ce wannan rikici ya kaure, inda aka yi ta jin kararrakin harbe harbe da fashe fashe daga babban birnin kasar.

Daga bisani a ranar Asabar din runduna ta musamman ta yi ikirarin karbe iko da filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Khartoum da sauran mahimman wurare.

Sai dai rundunar sojin Sudan ta musanta ikirarin, inda a wata sanarwa da ta fitar a daren Asabar take kira ga al’ummar da ke yankunan da abin ya shafa su kasance a cikin gidajensu a yayin da take ci gaba da luguden wuta a sansanonin dakarun na musamman din wato RSF.

Rikicin ya  barke ne  bayan da aka shafe makwanni ana zaman tankiya tsakanin jagoran gwamnatin sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, kuma kwamandan runduna ta musamman na kasar, Hamdan Daglo.

Runduna ta musamman ta RSF da aka kirkiro  a shekarar 2013 ta sao asali ne daga kungiyaar ‘yaan tsagerar Janjaweed, wadda tsohon shugaban kasar, Omar al-Bashir ya yi amafani da ita wajen muzgunawa ‘yan tsirarun kabilu wadanda ba Larabawa ba a yankin yammacin Darfur, lamarin da yanzu ya janyo masa tuhumar aikata laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.