Isa ga babban shafi

Masu zanga-zangar kin jinin mulkin Soja sun yi arangama da 'yan sanda a Sudan

An sake samun arangama tsakanin masu zanga-zanga a Sudan da jami’an tsaro yau laraba a birnin Khartoum zanga-zangar da ta sake tsananta a jiya duk dai aci gaba da nuna adawa da jagorancin Soji a kasar.

Wata zanga-zangar kin jinin Sojoji a Sudan.
Wata zanga-zangar kin jinin Sojoji a Sudan. AFP - EBRAHIM HAMID
Talla

Dubban masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa inda suke daga kwalayen da ke dauke da rubutun nuna kiyayya ga gwamnatin Sojin yayinda wasun s uke furtawa da baki cewa basa bukatar mulkin Soji a Kasara.

Masu zanga-zangar sun bayyan juyin mulkin bara karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan a matsayin babban kuskuren da ya sake jefa kasar a matsala.

Rahotanni sun bayyana cewa da dama daga cikin masu zanga-zangar sun jikkata bayan da jami’an ‘yan sandan suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye akansu.

Baya ga dandazon masu zanga-zangar da suka yi dafifi a birnin Khartoum shaidun gani da ido sun kuma bayyana yadda aka samu makamancin gangamin a biranen Wad Madani na kudancin Khartoum da kuma Gedaref na gabashi.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akalla mutane 370 suka mutu cikin shekarar nan a Sudan saboda rikice-rikice masu alaka da zanga-zangar kin jinin mulkin Soji yayinda wasu fiye da dubu 210 kuma aka tilasta musu barin matsugunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.