Isa ga babban shafi

Ana fargabar barkewar cututtuka a Sudan bayan gano wasu gawarwaki

Hukumomin lafiya a Sudan sun yi gargadin cewa sama da gawarwakin mutane 1,500  da aka tara a dakunan ajiye gawarwaki na kasar na iya haifar da barkewar cututtuka, a daidai lokacin da ake zargin gwamnati da boye musabbabin mutuwarsu.

Likitoci sun ce idan har ba a dauki matakan gaggawa ba, shakka babu za a samu barkewar cututtuka a sassan kasar
Likitoci sun ce idan har ba a dauki matakan gaggawa ba, shakka babu za a samu barkewar cututtuka a sassan kasar REUTERS/Emre Rende
Talla

Daga cikin wadanda suka mutun ana kyautata zaton akwai masu zanga-zangar adawa da mulkin soji, wadanda masu fafutuka suka ce dakarun gwamnati ne suka kashe su a yunkurinsu na murkushe zanga-zangar.

Khalid Mohamed Khaled, mai magana da yawun hukumar kula da lafiya ta gwamnati, ya bayyana damuwarsa saboda kusancin dakin ajiye gawarwaki da wata kasuwa, yana mai cewa gawarwakin na iya yada cutar kwalara da sauran cutukan da za su kasance masu yaduwa, a tsakanin mazauna yankin.

A wani taron manema labarai, ya nuna rashin amincewa da bukatar gudanar da bincike mai zaman kansa, inda ya ce a maimakon haka ya kamata a binne gawarwakin saboda kare lafiyar jama’a.

Rahotonni kan binciken musabbabin mutuwar mutanen ya fara bayyana ne a watan Mayu, inda faifan bidiyo da aka fitar a farkon wannan watan ya nuna tarin gawarwakin da aka ajiye a wani gini da alamu suka nuna cewa babu na'urar adana gawa a ciki.

Sannan babban mai shigar da kara na kasar ya ba da izinin binne gawarwakin a watan da ya gabata ba tare da tantance abin da ya kashe mutanen ba.

Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke murkushe masu zanga-zangar kin jinin sojoji bayan juyin mulkin da aka yi a bara.

A watan Oktoban da ya gabata, aka inganta tsarin mulkin demokradiyya a Sudan na dan gajeren lokaci, bayan da shugaba Abdel-Fattah Burhan, ya hambarar da gwamnati tare da kulle daruruwan mutane ciki har da masu fafutuka.

Kungiyoyin rajin kare demokradiyya da iyalan masu zanga-zangar da suka bata sun ce rashin gudanar da binciken wani yunkuri ne na boye shaidar kisan daruruwan masu zanga-zangar da sojojin Sudan suka yi, biyo bayan boren al'ummar kasar a shekara ta 2019 da ya hambarar da shugaba Omar al-Bashir.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kwamitin likitocin kasar Sudan da ke bin diddigin mutuwar masu zanga-zangar tun bayan juyin mulkin, suma suka gudanar da maci a wajen hedkwatar masu gabatar da kara.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta yi kira da a dakatar da duk wata jana'iza, har sai an kawo wata tawagar likitocin kasa da kasa, masu zaman kansu da kuma amintattun likitocin da ke kare hakkin wadanda suka bace, domin binciko gaskiyar da aka boye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.