Isa ga babban shafi

Ana wani sabon yukunri na kawo karshen rikicin Sudan

Jakadan Amurka a Sudan ya yi kira ga tsoffin ‘yan tawayen da ba sa cikin yarjejeniyar farko da aka kulla bayan juyin mulkin da su shiga tattaunawar da ake yi na maido da mulkin farar hula.

Wasu daga cikin kungiyoyin farreren hula na kasar Sudan
Wasu daga cikin kungiyoyin farreren hula na kasar Sudan © Marwan Ali / AP
Talla

Shugabannin soji da wasu kungiyoyin farar hula sun amince a watan da ya gabata kan matakin farko na tsarin siyasa mai matakai biyu na neman kawo karshen rikicin da Sudan ta fada tun bayan juyin mulkin shekarar 2021 karkashin jagorancin Hafsan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan.

Yayin da yarjejeniyar ta janyo hankalin kasashen Duniya, yan adawa na cikin gida suna masu cewa  gwamnatin ta gaza kan takamaiman lokaci a alkawuran da ta dauka ga jama’a.

Jakadan   Amurka John Godfrey ya sheidawa kamfanin dillancin labarai na AFP a jiya alhamis, yayin da yake magana kan wasu manyan bangarorin da suka ki sanya hannu kan yarjejeniyar, yana da muhimmanci a lura cewa tsarin yana nan a bude domin su shigo.

Tsohon madugun yan tawaye Mini Minnawi, gwamnan yankin Darfur mai fama da tashin hankali, ya yi Allah wadai da yarjejeniyar da cewa ta janye.

Ministan kudin kasar Gibril Ibrahim, wanda kuma tsohon shugaban yan tawaye ne, wanda ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin rikon kwaryar Sudan, ya na mai cewa abin da suka fahimta shi ne kokarin da ake yi na ci gaba da nemo hanyar da za a bi don tanttance hanyoyin da suka dace domin shiga wannan tsari, in ji Godfrey.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.