Isa ga babban shafi

Fada ya kaure tsakanin sojojin Sudan da runduna ta musamman

An ji karar fashe fashe a babban birnin Sudan, Khartoum a yau Asabar, sakamakon rikicin da ya kaure tsakanin dakaru na musamman da ke gadin fadar shugaban kasar da sojoji, kwanaki bayan da rundunar sojin kasar ta yi kashedin cewa kasar ta shiga wani matsayi mai hatsari.

Jagoran mulkin sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan .
Jagoran mulkin sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan . AP
Talla

Rikicin ya  barke ne  bayan da aka shafe maakwanni ana zaman tankiya tsakanin jagoran gwamnatin sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, kuma kwamandan runduna ta musamman na kasar, Hamdan Daglo.

Ganau sun ruwaito cewa an yi arangama, inda aka ji karar fashe fashe a kusa da ofishin runduna ta musamman, wato RSF.

Runduna ta musamman ta ce dakarunta sun karbe iko da filin jirgin sama na birnin Khartoum a halin da ake ciki, bayan da shaidu suka ce sun hangho motoci cike da mayaka na shiga cikin harabar filin jirgin saman.

Wakilan kamfanin dillancin labaran Faransa sun ruwaito cewa sun jiyo karar  harbe harbe a kusa da filin jirgin saman, da kuma kusa da gidan Burhan a arewacin birnin Khartoum.

An hango fararen hula suna ta tserewa don tsira da rayukansu.

Bangarorin biyu dai na zargin jina da  tada rikicin.

Jagoran mulkin sojin Sudan, Burhan da mataimakainsa suna cikin rashin jituwa ne a kan tattaunawar yarjejeniyar mika mulki ga farar hula tare da karshen rikicin da ya kunno kai tun bayan juyin mulkin shekarar 2021.

Runduna ta musamman ta RSF da aka kirkiro  a shekarar 2013 ta sao asali ne daga kungiyaar ‘yaan tsagerar Janjaweed, wadda tsohon shugaban kasar, Omar al-Bashir ya yi amafani da ita wajen muzgunawa ‘yan tsirarun kabilu wadanda ba Larabawa ba a yankin yammacin Darfur, lamarin da yanzu ya janyo masa tuhumar aikata laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.