Isa ga babban shafi

Adadin mamata a ambaliyar Sudan ya tasamman 112

'Yan sanda a Sudan sun ce adadin mutanen da ambaliyar ruwan bana ta kashe ya kai 112, yayin da ta rusa dubban gidaje da kuma raba dimbin mutane da gidajen su.

Yankin Kassala, na kasar sudan kenan da ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa
Yankin Kassala, na kasar sudan kenan da ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa ASHRAF SHAZLY / AFP
Talla

Mai magana da yawun rundunar Yan Sandan kasar, Abdel Jalil Abdelraheem ya gabatar da wannan adadi, yayin da ya kara da cewar gidaje dubu 34 da dari 944 sun rushe gaba daya, yayin da wasu dubu 49 da 060 suka ‘dan lalace.

Wannan iftila’i na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar rikicin siyasa, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar, abinda ya baiwa Janar Abdel Fatah al-Burhan mulki.

A makon jiya, Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewar adadin mutanen da ambaliyar ta shafa a Sudan ya kai dubu 226.

Hukumar UNICEF tace matsalar tafi kamari a Jihohin Gedaref da Kassala, sai kuma Arewaci da Kudancin Kordafan, tare da Jihar River Nile da kuma Yankin Darfur.

Hukumar tayi gargadin cewar matsalar ambaliyar na iya shafar mutanen da yawan su zai kai dubu 460, sabanin dubu 388 da aka gani tsakanin shekarar 2017 zuwa 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.