Isa ga babban shafi

Chadi ta ce 'yan Sudan 320 na gudun hijira a kasar

Gwamnatin kasar Chadi tace sojojin Sudan kusan 320 suka gudu daga yakin da ake fafatawa kasar su inda suka tsallaka iyaka zuwa cikin kasar ta domin kare lafiyarsu. 

Yadda mutane suka fara ficewa daga birnin Khartoum na kasar Sudan. An dauki hoton ranar 18, ga watan Afrilun 2023.
Yadda mutane suka fara ficewa daga birnin Khartoum na kasar Sudan. An dauki hoton ranar 18, ga watan Afrilun 2023. AP - Marwan Ali
Talla

Ministan tsaron Chadi, Janar Daoud Yaya Brahim ya bayyana shigar sojojin Sudan kasar su bayan barkewar yakin basasar kasar. 

Janar Brahim ya tabbatar da shigar sojojin 320 da kuma kwance damar su tare da tsare su a ranar lahadin da ta gabata, bayan sun shaida musu cewar sun gudu ne domin kaucewa kisa daga hannun dakarun dake goyan bayan mataimakin shugaban Sudan Mohammed Hamdan Daglo. 

Ministan ya bayyana halin da ake ciki a Sudan a matsayin abin tada hankali, yayin da yace Chadi ta dauki kwararan matakai domin kare iyakokin ta duk da yake yakin bai shafe ta kai tsaye. 

Tun a ranar asabar Chadi ta rufe iyakokin ta da Sudan wanda tsayin sa ya kai sama da kilomita 1,000 wanda yan tawayen kasashen biyu kan yi amfani da shi suna kai hari. 

Dubban fararen hula ne suke ta barin birnin Khartoum inda rikicin ya fi kazancewa domin kaucewa fadan da ake gwabzawa da manyan makamai cikin su harda jiragen yaki da kuma makaman atilare. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.