Isa ga babban shafi

Sudan ta yi tir da harin 'yan bindigar Chadi da ya kashe ma ta mutane 18

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta yi tir da harin da wata kungiya mai rike da makami a Chadi ta kai tare da kashe mutane 18 ‘yan Sudan 18.

Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke jagorancin gwamnatin Sojin Sudan.
Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke jagorancin gwamnatin Sojin Sudan. AFP - ASHRAF SHAZLY
Talla

Kafofin labaran Sudan sun ruwaito cewa a alhamis din da ta gabata ne harin ya faru lokacin da wata tawagar makiyaya daga yammacin Darfur ke bin sahun wasu ‘yan bindiga barayin rakuma da suka fito daga Chadi.

A cewar bayanai ‘yan bindigar sun yiwa makiyayan kwantan bauna tare da afkwa musu wanda ya kai ga kisan mutum 18 a cikinsu kwana guda bayan yi musu fashin tarin rakuma.

A asabar din da ta gabata, mukaddashin ministan harkokin wajen Sudan Al- al-Sadiq ya jagoranci tawagar gwamnati wajen ganawa da jakadan Chadi a Khartoum tare da bayyana bacin ransa kan harin.

Haka zalika ministan ya bukaci mahukuntan Chadi su yi dukkanin mai yiwuwa wajen kame maharan tare da dawo da abin da suka sata baya ga yi musu hukunci dai dai da laifinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.