Isa ga babban shafi
RIKICIN-SUDAN

Sudan tace hankali ya fara kwanciya bayan rikici tsakanin Hausawa da Berti

Gwamnatin Sudan tace hankali ya fara kwanciya bayan rikicin kabilanci tsakanin Hausawa da Yan Kabilar Berti a Jihar Blue Nile wanda yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 100, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban daban.

Shugaban Sudan Janar Abdel Fatah al-Burhan
Shugaban Sudan Janar Abdel Fatah al-Burhan © ASHRAF SHAZLY/AFP
Talla

Rahotanni sun danganta barkewar rikicin da bukatar al’ummar Hausawan na mallakar filaye da masarauta tare da kuma damawa da su a cikin harkokin gwamnati, yayin da abokan zaman su ke kallon su a matsayin baki wadanda ba ‘yan kasar ba, bayan kwashe shekaru da dama suna zama a kasar.

Rahotanni sun ce akasarin Hausawan dake Sudan sun samo assali ne daga Hausawan Najeriya da suka fito daga Jihohin Sokoto da Katsina da Kano wadanda kakanin su suka tafi akin Hajji da kafa abinda ke sanya su ratsawa ta kasar Sudan kafin tsallaka teku.

Wasu daga cikin Yan gudun hijira sakamakon rikicin da aka samu
Wasu daga cikin Yan gudun hijira sakamakon rikicin da aka samu AFP - -

Bayanai sun ce wasu daga cikin matafiyan kan yada zango a Sudan kafin su isa Makkah ko kuma lokacin dawowa daga aikin Hajjin, abinda sannu a hankali yayi sanadiyar zaman su a kasar.

Masana tarihi sun kuma danganta zaman Hausawan a Sudan da gudun hijirar da Sarkin Musulmin Najeriya yayi a shekarar 1903 bayan da Turawan mulkin mallaka suka samu galaba karbe iko a shekarar 1903.

Daya daga cikin matasan da suka shiga zanga zangar da akayi a makon jiya a biranen Gedaref da Kassala da kuma Port Sudan tare da El Obeid, domin bukatar ganin gwamnati ta kaddamar da bincike domin bin Kadin mutane sama da 100 da aka kashe a Jihar Blue Nile Malam Umar Hamza Abdullahi ya shaidawa RFI Hausa cewar bayan kwashe dogon lokaci Hausawa na zama a kasar Sudan har yanzu ana musu kallon su ba ‘yan kasa bane, duk da arzikin da suke da shi da kuma gudumawar da suke bayarwa wajen ci gaban kasa.

Wasu daga cikin wadanda suka rasa gidajen su sakamakon rikicin da aka samu a Jihar Blue Nile
Wasu daga cikin wadanda suka rasa gidajen su sakamakon rikicin da aka samu a Jihar Blue Nile AFP - ASHRAF SHAZLY

Abdullahi yace duk da yake basu cika shiga ayyukan gwamnati ko na jami’an tsaro ba, suna bada gudumawa sosai wajen ci gaban kasar musamman abinda ya shafi tattalin arzikin kasa.

Bukatar Hausawa na kafa Masarauta da kuma mallakar filaye da sabon Gwamnan Jihar Blue Nile ya basu domin sanya cikin gwamnati da kuma bada damar damawa da su ya harzuka Yan kabilar Berta, wadanda suke kallon matakin a matsayin barazana ga shugabancin su a yankin, abinda ya kaiga artabu a tsakanin su da kuma rasa rayuka.

Ministan lafiyar kasar Jamal Naseer wanda ya tabbatar da mutuwar mutane 105 da kuma jikkata 291 a rikicin, yace an tura karin sojoji da Yan Sanda domin tabbatar da tsaro, kuma hankali ya fara kwanciya.

Majalisar Dinkin Duniya tace mutane sama da 17,000 suka tsere daga gidajen su sakamakon rikicin, yayin da yanzu haka 14,000 suka samu mafaka a wasu makarantu dake al-Damazin.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da suke tsere daga muhallansu saboda rikicin yankin Tigray.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da suke tsere daga muhallansu saboda rikicin yankin Tigray. AP - Nariman El-Mofty

Sai dai shugaban Hausawan Mohammed Noureddine yace adadin mutanen da aka kasha na iya tashi, ganin cewar akwai wadanda suka bata da dama, yayin da burabuzan gine gine suka birne wasu daga cikin su.

Wani daga cikin shugabannin Hausawan Hafez Omar ya zargi gwamnati da goyan bayan ‘Yan kabilar Berta saboda abinda ya kira yadda akayi amfani da makaman gwamnati wajen afka musu.

Sai dai wani shugaban ‘Yan Kabilar Berti ya musanta zargin, inda yace sun shiga fadan ne domin kare filayen su daga saboda saba dokokin yankin da Hausawa suka yi.

Majalisar Dinkin Duniya tace tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekarar, ta aikewa mutane 563,000 agaji a Jihar Blue Nile wanda ke kokarin murmurewa daga tashe tashen hankulan da aka samu a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.