Isa ga babban shafi

Rikicin kabilanci ya yi hallaka mutane 33 a wani yanki na Sudan

Hukumonin Sudan sun kafa dokar hana fitar dare a wani yankin jihar Blue Nile jiya Asabar, sakamakon ci gaba da gwabza fada da ake yi tsakanin kabilun yankin biyu da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 33, yayin da daruruwan mutane ne suka  tsarewa tashin hankalin.

Wasu mutane dake kauracewa rikicin Sudan, Satumban 2011.
Wasu mutane dake kauracewa rikicin Sudan, Satumban 2011. CRISIS GROUP/Jérôme Tubiana
Talla

Akalla wasu 108 kuma sun jikkata a cewar sanarwar da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar, kana shaguna 16 sun kone tun bayan tashin hankalin da ya barke a ranar litinin sakamakon rikicin filaye tsakanin 'yan kabilar Berti da Hawsawa.

Wani jami’in yankin Abdel Agar  ya koka kan karancin jami’an tsaro. A cewarsa, mutane da dama na neman mafaka a ofisoshin 'yan sanda kuma tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Shiga tsakani

Agar dai bai bayar da cikakken bayani ba amma ya ce ana bukatar masu shiga tsakani cikin gaggawa domin dakile tashe tashen hankula.

An tura sojoji domin shawo kan lamarin kuma hukumomi sun kafa dokar hana fitar dare daga ranar Asabar.

Haramta taruka

Gwamnan Blue Nile Ahmed al-Omda ya ba da umarnin a ranar Juma'a da ta haramta duk wani taro ko tattaki na tsawon wata guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.