An kashe sama da mutane 200 a rikicin kabilanci a Sudan
Akalla mutane 213 ne aka kashe a rikicin da aka kwashe kwanaki 3 ana yi tsakanin Larabawa da sauran kabilu a yammacin yankin Darfur na Sudan.
Wallafawa ranar:
Yammacin yankin Darfur ya tsunduma cikin rikici da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa a Krink, wani kauye mai yawan mutane kusan dubu 500, inda aka fi samun ‘yan kabilar Massalit, kuma gwamnan jihar Khamees Abkar ya tabbatar da yawan mutanen da suka suka mutu a wani faifen bidiyo.
A ranar Juma’a da ta gabata ne rikici ya fara barkewa, ya kuma ta’azzara a lokacin da wasu, dauke da makamai suka afka wa kauyukan wadanda ba Larabawa ba a matsayin ramuwar gayya ga kisan wasu mutanensu biyu da aka yi.
A ranar Talata, kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta Medecins Sans Frontiere ta ce an kashe ma’aikatan lafiya da dama a rikicin saboda hare hare da aka kai wa asibitoci.
Rikicin Darfur da aka fara a shekarar 2003, yayi sanadin mutuwar sama da mutane dubu 300 tare da daidaita miliyan 2 da rabi a cewar majalisar dinkin duniya.
Wannan rikici na baya bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da Sudan ke kokarin girgijewa daga matsalar da juyin mulki da jagoran soji, Abdel Fattah al-Burham ya jagoranta a watan Oktoban 2021.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu