Isa ga babban shafi

Hausawa sun kai hari kan gine-ginen gwamnati a Sudan

Daruruwan al'ummar Hausawa a Sudan sun kafa shingaye tare da kai hari kan gine-ginen gwamnati a garuruwa da dama na kasar, kamar yadda shaidu suka bayyana, bayan shafe mako guda ana rikicin kabilanci a kasar.

Masu zanga-zanga a Sudan.
Masu zanga-zanga a Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

A wani yunkuri na nuna bacin rai game da rikicin  da ya barke a jihar Blue Nile, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 79 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana, al’ummar Hausawa sun yi kiran gudanar da zanga-zanga a Talatar nan a birnin Khartoum na kasar ta Sudan.

Rikici tsakanin kabilar Berti da Hausawa, ya barke ne a ranar Litinin din makon jiya, bayan da ‘yan kabilar Bertis suka ki amincewa da bukatar da Hausawa suka gabatar ta samar da shugabancinsu da zai kula da yadda ake samun filaye, kamar yadda wani fitaccen Bahaushe da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Sai dai wani jigo a kabilar Bertis ya ce, kabilarsu na mayar da martani ne ga wuce gona da irin da Hausawa suka yi musu.

Ma'aikatar Lafiyar yankin ta ce, adadin wadanda suka mutu a rikicin ya kai 79 sabanin 60 da a baya aka bayyana, yayin da ta ce, adadin wadanda suka jikkata 163 ne sabanin 199, da aka bayyana.

Al’ummar Hausawa da ke zaune a Sudan sun kai miliyan uku, inda suke amfani da harshensu na asali maimakon Larabci.

Yawancinsu suna rayuwa ne ta hanyar noma a yankin Darfur, da jihar Al-Jazira da kuma jihohin Kassala da Gedaref da Sennar da kuma Blue Nile.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.