Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a rikicin kabilancin Sudan ya kai 60

Rikicin kabilanci dan aka yi a yankin kudancin jihar Blue Nile  a kusa da iyakar Sudan da Habasha, ya yi sanadin mutuwar mutane 60 tare da jikkata 163 ya zuwa yanzu, a cewar ma’aikatar lafiyar sudan din.

Yankin Darfu a cikin Sudan
Yankin Darfu a cikin Sudan Reuters/路透社
Talla

Kamfanin dillancin labarn Faransa ya ruwaito cewa 13 daga cikin wadanda suka jikkata suna cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai, kuma za a garzaya da su zuwa asibitoci a birnin Khartoum.

A ranar Asabar ce hukumomi suka ayyana dokar hana fitar dare a yankuna da ake gwabza rikicin kabilancin tsakanin wasu kabilu 2.

An kona shaguna 16  tun bayan tashin rikicin da ya kunno kai sakamakon takaddama a kan filaye tsakani kabilar Berti da Hausawa a ranar Litinin da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.