Isa ga babban shafi

Masu zanga-zangar Sudan sun rufe sansanoninsu biyu

Masu shirya zaman dirshan a Khartoum da ke Sudan, da suka fara gwagwarmayar kwanaki 10 da suka gabata domin tilastawa sojojin kasar mayar da mulki hannun farar hula, sun sanar da janye biyu daga cikin sansanoninsu guda hudu.

Wani yankin birnin Khartoum da ya fuskanci taron masu zanga-zangar. adawa da sojoji.
Wani yankin birnin Khartoum da ya fuskanci taron masu zanga-zangar. adawa da sojoji. AP - Marwan Ali
Talla

A cewar masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya a kasar, zanga-zangar da aka faro ta a ranar 30 ga watan Yuni bayan da jami'an tsaro suka kashe masu zanga-zanga tara, ita ce mafi muni a wannan shekarar.

Masu zanga-zangar dai, sun kafa sansanoni hudu biyu a tsakiyar birnin Khartoum akan tituna, sannan kuma guda guda a manyan biranen Omdurman da Khartoum ta Arewa.

Sai dai a ranar litinin din nan, kwamitocin adawar sun sanar da wargaza sansanin Omdurman.

Dama kuma a ranar Juma’a ne aka dage zaman dirshan a wajen asibitin al-Jawda na birnin Khartoum.

Zanga-zangar da aka yi a ranar 30 ga watan Yuni da zaman dirshan da suka biyo baya ya nuna sake bullar zanga-zangar neman mulkin farar hula. Duk da cewa kungiyar ta ci gaba da gudanar da tarukan adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.