Isa ga babban shafi

Sabuwar zanga-zanga ta barke a Sudan bayan kisan fararen hula 9

Al’ummar Sudan sun sake kwarara kan titunan kasar yau juma'a a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Soji da ke shiga rana ta biyu, zanga-zangar da ke zuwa duk da kisan fararen hular da ake zargin jami'an tsaron kasar da yi a makamantan gangamin da suka gabata a baya.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Soji a birnin Khartoum na Sudan.
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Soji a birnin Khartoum na Sudan. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

A alhamis din da ta gabata ne al'ummar Sudan suka faro sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnatin Sojin bayan kisan mutane 9 yayinda jami’an tsaro ke ci gaba da harba hayaki mai sa hawaye a kokarin da su ke yi na tarwatsa masu zanga-zangar.

Bayanai na cewa dubban masu zanga-zangar a karkashin jagorancin masu gwagwarmayar tabbatar da mulkin dimokradiyya a kasar ne suka mamaye fadar shugaban kasar a birnin Khartoum dalilin da ya sanya jami'an tsraon kisan fararen hula 9.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa masu zanga-zanagar na rike da kwaleyen da suka rubuta "Dole mu kawo karshen mulkin Al-Burhan" da kuma hotunan mutanen da aka kasha a zanga-zangar da da ‘yan kasar ke yi akai-akai tun hambarar da gwamnatin Omar Al-Bashir.

Tun daga Juyin Mukin bara zuwa yanzu an kashe masu zanga-zanga 113, dalilin cinkoso, harbin jami’an tsrao da sauran dalilai.

Babbar bukatar masu zanga-zangardai itace mayarda mulkin kasar hannun farar hula, wanda dama a 2019 ya koma hannun Omar Al-Bashir daga Sojojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.