Isa ga babban shafi

AU ta yi barazanar juya wa tattaunawar Sudan baya

Kungiyar tarayyar Africa, ta ce babu gudun mowar da za ta iya bayar wa kan kowacce irin tattaunawa da ta shafi Sudan game da batun tsarin mulkin farar hula, matukar aka ki sanya masu ruwa da tsaki cikin lamuran.

Shugaban gwamnatin sojan Sudan kenan, Abdel Fattah al-Burhan.
Shugaban gwamnatin sojan Sudan kenan, Abdel Fattah al-Burhan. AFP PHOTO/HO/SUNA
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da tattaunawa don ganin an mayar da Sudan bisa tsarin mulkin dimokradiyya bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a shekarar 2021.

Tuni wasu daga cikin kungiyoyin Fararen hula a Sudan din, suka fara kaurace wa taron su da sojojin da ke rike da ikon kasar a farkon makon nan karkashin sanya idanun manyan hukumomi na duniya.

tun a shekarar 2021 Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Sudan daga cikin ta, sakamakon juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin tsohon shugaba Omar Al-Bashir, tare da kafa gwamnatin hadaka.

Wannan ta sa manyan kasashen duniya da hukumomin kudi suka janye duk wani tallafi da suke bawa kasar da sama da kaso 40 cikin dari, abinda ya tilastawa gwamnatin sojin kasar, karkashin Abdel Fatah Al-Burhan ta amince da shiga tattaunawar mika mulki ga hannun farar hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.