Isa ga babban shafi

An fara zaman magance rikicin siyasar Sudan

Bangarorin da ke hamayya da juna a Sudan sun fara tattaunawar keke da keke karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya domin warware rikcin siyasar kasar da ya ta’azzara biyo bayan juyin mulkin soji a bara.

Masu zanga-zanga a Sudan.
Masu zanga-zanga a Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Sai dai rahotanni na cewa, wani bangaren fararen hula mai muhimmancin gaske ya kaurace wa zaman sasantawar.

Tun bayan juyin mulkin soji ne, kasar ta Sudan ta tsunduma cikin jerin rikita-rikita, inda jama’a ke gudanar da zanga-zanga kusan kowanne mako, yayin da jami’an tsaro suka kashe sama da mutane 100 a kokarin murkushe masu boren.

Kazalika kasar ta fuskanci tabarbarewar tattalin arziki.

A yayin kaddamar da zaman tattaunawar a birnin Khartoum, daruruwan mutane sun yi fitar-dango a yankin gabashin birnin, suna masu kira da a kafa gwamnatin farar hula zalla.

Dan jaridar Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya rawaito cewa, jami’an tsaro sun cilla hayaki mai sa-kwalla domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a taron, Volker Perthes ya shaida wa manema labarai cewa, yana da matukar muhimmmaci a ribaci wannan lokacin na sasantawar, yana mai kira ga dukkanin bangarorin da su yi zaman da kyakkyawar niyya.

Juyin mulkin da sojin suka yi, shi ne ya sukurkuta shirin mika mulki ga farar hula wanda aka tsara tun bayan kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekara ta 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.