Isa ga babban shafi

Dangantakar diflomasiyya na neman tsami tsakanin Sudan da Habasha

Sudan ta ce za ta kira jakadanta da ke Addis Ababa bayan zargin sojojin Habasha da kashe sojojin Sudan bakwai da aka kama da wani farar hula guda, tare da cewa za ta mika korafin ta ga kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya.

Shugaban mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan 2021.
Shugaban mulkin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan 2021. AFP - ASHRAF SHAZLY
Talla

An samu tashin hankali a shekarun baya-bayan nan, wanda ya haifar da kazamin fada, a kan iyakar Al-Fashaqa, da ke kusa da yankin Tigray na kasar Habasha mai fama da rikici.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga gwamnatin kasar ta Habasha game da zargin sojojin na Sudan.

Wani jami’in sojan Sudan da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an tsare sojojin ne a wani yanki da ke kan iyaka da yankin Al-Fashaqa.

Gwamnatin Sudan ta ce za a gayyaci jakadan Habasha a Khartoum domin sanar da shi yadda Sudan ta yi Allah wadai da wannan ta'asar da sojojin kasarsa suka aikata.

Dangantaka tsakanin Sudan da habasha ta yi tsami a kan Al-Fashaqa, wani yanki mai albarka da manoman Habasha suka dade suna noma  a wurin amma Sudan ta yi ikirarin karbewa, lamarin da ya haifar da kazamin fada tsakanin bangarorin Sudan da Habasha, haka kuma tashin hankalin da ya barke a yankin Tigray a watan Nuwamban 2020 ya tilastawa dubun dubatar ‘yan gudun hijirar Habasha tserewa zuwa Sudan din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.