Isa ga babban shafi
Habasha

Habasha ta fara samar da wutar lantarki a madatsar ruwan Nilu duk da cece-kuce

Kasar Habasha ta fara samar da wutar lantarki daga babbar madatsar ruwa da ke kogin Nilu a jiya Lahadi,  bayan tsawon shekaru da aka dauka ana takaddama kan aikin gina madatsar ta biliyoyin Dala.

Franministan Habasha Abiy Ahmed yayin kaddamar da madatsar ruwan kogin Nilu, 20/02/22.
Franministan Habasha Abiy Ahmed yayin kaddamar da madatsar ruwan kogin Nilu, 20/02/22. Amanuel SILESHI AFP
Talla

Firaministan Habasha Abiy Ahmed da ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnatinsa, ya yi rangadi a tashar madatsar ruwan, inda ya yi ta danna wasu madannai na latironi, abin da ake kallo a matsayin mafarin samun wutar lantarki daga wannan dam.

Wannan madatsa ta GERD za ta zama mafi girma a nahiyar Afrika wajen samar da wutar lanmtarki daga kogi, amma kasashen Masar da Sudan sun jima suna haifar da tarnaki a aikin gina madatsar wadda aka fara aza tubalinta tun shekara ta 2011.

Madatsar ruwan kogin Nilu da Habasha ta gina don samarwa al'ummarta wutan lantarki, sai dai Masar da Sudan na adawa da shirin.
Madatsar ruwan kogin Nilu da Habasha ta gina don samarwa al'ummarta wutan lantarki, sai dai Masar da Sudan na adawa da shirin. - Ethiopian Public Broadcaster (EBC)/AFP/File

A yayin kaddamar da madatsar ranar Lahadi, Firaminista Abiy ya bayyana ranar a matsayin wani sabon babin rayuwa.

Sudan da Masar

A cewarsa, wannan labari ne mai dadi ga nahiyar Afrika da suka hada da kasashen na Masar da Sudan da ya ce, yana fatan yin aiki tare da su.

Kasar Habasha dai, ta yi amanna cewa, gina madatsar na da matukar muhimmanci ga bangaren samar da wutar lantarkinta da kuma bunkasar  kasar wadda ita ce ta biyu mafi girma a Afrika.

Sai dai Masar da Sudan har yanzu, suna fargabar cewa, madatsar za ta zame musu barazana ta fuskar kustawa cikin kogin Nilu domin gudanar da nasu sha’anin, ammada gwamnatin Habasha ta yi watsi da wannan fargaba tasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.