Isa ga babban shafi
RIKICIN-KOGIN NILU

Kasashen Larabawa sun bukaci MDD ta sasanta rikicin kogin Nilu

Kungiyar Kasashen Larabawa ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gaggauta shiga tsakanin wajen warware rikicin dake ruruwa tsakanin kasashen Masar da Sudan da kuma Habasha dangane da gina madatsar ruwan da Habasha keyi akan kogin Nilu.

Shugaban kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta Arab League Ahmed Gheit
Shugaban kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta Arab League Ahmed Gheit AP - Hussein Malla
Talla

Sakataren kungiyar Ahmed Aboul Gheit ya bayyana haka bayan wani taro da ministocin kasashen dake kungiyar suka gudanar a Doha dake kasar Qatar kamar yadda kasashen Masar da Sudan suka bukata.

Kasar Habasha na fatar ganin madatsar ruwan da take ginawa wanda zai samu kashi 90 na ruwan sa daga Kogin Nilu ya taimaka mata wajen bunkasa tattalin arzikin ta ta hanyar noma da samar da wutar lantarki, yayin da kasashen Masar da Sudan ke cewa gina madatsar zai hana kasashen su samun ruwan da suke bukata.

Bayan kammala taron da ya samu halartar ministocin kungiyar 17, Sakatare Janar Aboul Gheit ya bayyana shirin samun ruwan kasashen Masar da Sudan a matsayin shirin tsaron kasashen Larabawa baki daya.

Ministocin Kasashen Larabawa
Ministocin Kasashen Larabawa © [Karim Jaafar/AFP]

Ministan harkokin wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani yace daukacin kasashen da suka halarci taron sun dauki matakin bai daya wajen goyawa Masar da Sudan baya cikin takaddamar.

Al Thani yace sun tattauna batun shiga tsakani kan gina madatsar ruwan da Habasha keyi da zummar ganin an warware matsalar ba tare da wani bangare ya cutu ba.

Ministan yace sun tattauna batun kaucewa goyan bayan wani bangare domin ganin kasashen dake kungiyar basu samu matsala ba.

Taron ministocin kasashen Larabawa a Doha
Taron ministocin kasashen Larabawa a Doha © AFP

Kasashen Sudan da Masar sun amince a wannan wata suyi aiki tare wajen janyo hankalin Habasha dangane da shirin da take yi na cike madatsar ruwan bayan katsewar shiga tsakanin kungiyar kasashen Afirka ta AU ba tare da sasanta bangarorin ba.

Kasashen biyu sun kuma bukaci kasar Amurka da Kungiyar kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya da su shiga cikin masu sasanta rikicin tare da kungiyar kasashen Afirka wadda take ta kokari akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.