Isa ga babban shafi
Sudan - Habasha

Mayakan sa-kai sun kashe dakarun Sudan a kan iyakarsu da Habasha

Rundunar sojin Sudan ta ce an kashe dakarunta da dama a wani hari da mayakan sa-kai dake da alaka da sojojin Habasha suka kai a wani yankin kan iyakar kasashen biyu mai arzikin kasa da suke takaddama a kai.

Sojojin Sudan da Masar yayin atasayen hadin gwiwa a yankin Um Sayyala, arewa maso yammacin Khartoum, a ranar 3 ga Mayu, 2021.
Sojojin Sudan da Masar yayin atasayen hadin gwiwa a yankin Um Sayyala, arewa maso yammacin Khartoum, a ranar 3 ga Mayu, 2021. © AFP
Talla

Dangantaka tsakanin Sudan da Habasha dai ta yi tsami a kan yankin Al-Fashaqa dake kan iyakokinsu, inda manoman Habasha suka dade suna nomawa, wanda Sudan ke ikirarin mallakinta ne.

Rundunar sojin Sudan ta ce Dakarunta da mayakan a kan masu alaka da Habasha suka kaiwa farmaki, na tsaka da aikin tabbatar da girbin amfanin gona ne a yankin na Al-Fashaqa, sai dai sojojin na ta sun yi nasarar dakile harin ko da yake sun rasa mazan fama da dama.

Har yanzu dai kasar Habasha ta ce komai akan lamarin ba.

Al-Fashaqa dake makwabtaka da yankin Tigray na kasar Habasha mai fama da rikici, ya sha fama da kazamin fada tsakanin dakarun Habasha da Sudan tsawon shekaru da suka gabata, rikicin da ya kara yin kamari a shekarar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.