Mutane biyar aka kashe a Sudan yayin zanga-zangar neman kawo karshen Gwamnatin soji
Akalla mutane biyar ne aka kashe a Sudan a lokacin da sojoji ke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar neman kawo karshen mulkin sojoji a kasar a birnin Kharthoum.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewar jami’an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar, wacce itace ta baya-bayan nan da aka gudanar don nuna rashin gamsuwa da mulki sojoji a kasar cikin watanni 8.
Jami’an kiwon lafiya sun ce mutane biyu daga cikin wancan adadin sun mutune ta sanadiyar harbi kai tsaye a kirjin su, lamarin da ya sa adadin masu zanga-zangar da aka kashe a cikin watanni ya kai dari da biyar.
Kamfanin dillancin labaran na AFP ya kuma ruwaito cewar, an katse internet da kuma layukan waya a safiyar alhamis din nan, a wani mataki da hukumomin Sudan ke amfani da shi wajen hana fitowar mutane da dama wajen zanga-zanagr.
An kuma tsaurara matakan tsaro a Khartom duk da dage dokar tabaci da aka sanya a birnin bayan gudanar da juyin mulki, inda sojoji da ‘yan sanda suka rufe duk wasu hanyoyi da ke zuwa shalkwatar sojoji da kuma fadar shugaban kasar.
Jakadan majalisar dinkin duniya a kasar Volker Perthes da kuma ofishin jakadancin Amurka, sun bukaci a takaita rikicin da kuma baiwa fararen hula kariya don gudun rasa rayuka.
Sudan dai ta shiga cikin rudani ne ta hanyar zanga-zanga, bayan da tattalin arzikin kasar ya tabarbare a karkashin jagorancin Burhan da ya kwace mulki a shekarar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu