An bukaci Sudan ta gagguta bincike kan kisan masu zanga-zanga
Wani jami’in hukumar kare hakin dan adam ta majalisar dinkin duniya ya yi kira ga hukumomin Sudan da su gaggauta bincike a kan kisan masu zanga zang da sauran manyan laifuka da ake aikatawa a kasar, a daidai lokacin da adadin mutanen da aka kashe tun da sojoji suka karbe mulki a shekarar da ta gabata ya kai 100.
Wallafawa ranar:
Adam Dieng ya shaida wa manema labarai cewa abin takaici ne ganin yadda mutane kusan dari suka mutu, sama da dubu 5 suka jikkata sakamakon amfani da karfi fiye da kima da jami’an tsaron kasar ke yi a kan fararen hula.
Sudan ta fada cikin tashin hankali tun bayan juyin mulki, ga kuma dirar mikiya a kan masu zanga zanga da sojoji ke yi tun lokcin da kwamndan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da kwace gwamnatin kasar a ranar 25 ga watan Oktoba, lamarin da ya ya kawo tsaiko a kokarin da ake na mika mulki ga fara hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu