Isa ga babban shafi

Sudan ta saki jagororin jam'iyyar Communist kwana guda bayan kamensu

Mahukuntan Sudan sun sanar da sakin jagororin masu adawa da mulkin Soji na jam’iyyar Communist, kwana guda bayan kame su da jami’an tsaro suka yi.

Sudan na ci gaba da fuskantar kakkarfar zanga-zanga daga masu adawa da mulkin Soja.
Sudan na ci gaba da fuskantar kakkarfar zanga-zanga daga masu adawa da mulkin Soja. AP - Marwan Ali
Talla

A jiya alhamis ne jami’an tsaro suka kame Mohammed Mukhtar al-Khatib shugaban jam’iyyar Communist, tare da wasu mutane biyu wadanda aka tsaresu tsawon dare guda gabanin sakinsu a safiyar yau juma’a.

Wata majiya ta ce matakin kamen jagororin na da nasaba da yadda shugabancin jam’iyyar ya yi wata ganawa da jagoran ‘yan tawayen kasar Abdel Wahid Nour wanda ya ki amincewa da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Sudan ta gabatar masa a 2020.

Tun bayan juyin mulkin Soji na watan Oktoba Sudan ta fada cikin zanga-zangar kin jinin gwamnati wanda ya kai ga kisan fararen hula 95 baya ga jikkata daruruwa.

Wasu bayanai sun ce zuwa yanzu dubban mutane jami’an tsaron Sudan suka kame a tsawon watanni da aka shafe ana zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.