Isa ga babban shafi
Sudan

Sojin Sudan sun saki mutane 115 cikin masu zanga-zangar kasar da aka kame

Majalisar Sojin Sudan ta sallami akala mutane 115 da ake tsare da su  biyo bayan shiga zanga-zangar kyamar hukumomin. Kasashen Duniya na ci gaba da kira ga hukumomin  soji na Sudan na ganin sun yi sassauci wajen tafiyar da ragamar iko.

Masu zanga-zangar Sudan.
Masu zanga-zangar Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Hukumomin  Sudan  sun salami  mutane 115 da aka tsare da su tsawon makonni a kurkuku bayan samu su da laifi shiga zanga-zangar kyamar majalisar sojin kasar.

Akasarin mutanen da aka sallama na aiki ne da kuyngiyoyin  kare hakokin bil Adam na wannan kasa da ta fada  rikicin siyasa tun bayan juyin mulkin da yayi gaba da gwamnatin Omar El Beshir.

Ana tsare da  akasarin masu rajin kare hakkokin bil Adam  ne ba tareda an zartas musu da hukunci ko tuhumar su da wani laifi a hukumance.

Majalisar sojin kasar ta sako wadanan mutane ne a wani lokaci da ya zo dai-dai da ziyarar manzon Majalisar dimkin Duniya da zai share kwanaki biyar a kasar ta Sudan.

Adama Dieng da sunan majalisar dinkin Duniya  sashen dake kula da kare hakkokin bil Adam zai ganawa da majalisar sojin kasar,kazzalika zai yi amfani da wannan dama inda zai haduwa da wakilan kungiyoyin kare hakkokin bil Adam a Sudan,hanyar da zai yi amfani da ita domin sauraren wasu daga cikin koken su,musaman  neman yanci gudanar da zanga-zanga da  incin fadar albarkacin bakin su.

A watan yuni na wannan shekara ne manzon na Majalisar Dimkin Duniya dan kasar Senegal Adama Dieng zai gabatar da sakamakon bincike da aka yi a kasar biyo bayan kisan mutane 82 yayin zanga-zangar kyamar hukumomin wuccin gadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.