Isa ga babban shafi
Sudan

Jami'an tsaro sun kame jagororin masu adawa da juyin mulki a Sudan

Jami'an tsaro a kasar Sudan sun kama jagororin adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi wadanda ke wallafe wallafe a intanet cikin su har da tsohon minista daga kungiyar FFC ta fararen hula.

Zanga-zangar adawa da juyin mulki a Sudan.
Zanga-zangar adawa da juyin mulki a Sudan. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Wadannan mutane na daga cikin n abaya bayan nan da hukumomin kasar suka kama tun bayan juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktobar bara wanda shugaba Abdel Fattah al-Burhan ya karbe iko.

Rahotanni sun ce Yan Sandan farin kaya sun kama tsohon ministan Omar Youssef lokacin da yake jagorancin taro tare da Mohammed Hassan Arabi, wani babban jami’I a Jam’iyyar Congress Party.

Kama wadannan mutane na zuwa ne kwana guda bayan da wasu mutane biyu suka shiga tawagar da ta gana da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Volker Perthes dake jagorancin yunkurin sasanta rikicin siyasar kasar.

Babban dan adawar kasar Yaseer Arman yace kama wadannan mutane na iya yin illa ga tattaunawar zaman lafiyar da Majalisar ke jagoranci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.