Isa ga babban shafi

Sudan ta haramtawa Al Jazeera ci gaba da aiki a kasar

Hukumomin kasar Sudan  sun sanar da janye izinin da suka baiwa tashar talabijen ta kasar Qatar  Al Jazeera.Indan aka yi tuni jim kadan da juyin mulkin soji na ranar 25 ga watan Oktoba a Sudan ,yan sanda sun kama wakilin tashar Al Jazeera da wasu manema labarai dake aiki a wannan kasa.

Taron masu zanga-zanga a Sudan
Taron masu zanga-zanga a Sudan AFP/Yasuyoshi Chiba
Talla

A lokacin ,ana zargin tashar ta Al Jazeera da yada labaren karya da wasu tsofin faya-faye bidiyo da nufin haifar da rudani a wannan kasa.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Sudan © AFP

A jiya asabar ne Ministan yada labaren kasar ta Sudan ya aike da wasika da nufin sanar da shugabanin tashar cewa ,ba su da izinin ci gaba da aiki a wannan kasa,wata majiya na zargin tashar da nuna wani bidiyo da ga duk alamu zai iya tunzura jama’a ga tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.