Isa ga babban shafi
Sudan

Sojojin Sudan za su fice daga siyasa bayan zaben 2023 - Burhan

Shugaban gwamnatin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce sojoji za su fice daga harkokin siyasar kasar bayan zaben da aka shirya yi a shekara ta 2023.

Shugaban gwamnatin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan.
Shugaban gwamnatin sojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan. ASHRAF SHAZLY AFP
Talla

Yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Al-Burhan ya kara da cewa korarriyar tsohuwar jam'iyya mai mulki a kasar ta Sudan wato NCP ba za ta samu matsayi a gwamnatin rikon kwarya ba.

A ranar 25 ga watan Oktoba, Burhan ya kafa dokar ta baci, ya hambarar da gwamnatin kasar tare da tsare Firaminista Abdalla Hamdok, matakin da ya kara dagula tsarin mulkin farar hula a Sudan.

Juyin mulkin dai ya haifar da tofin A tsine da daukar matakan ladabtarwa daga gwamnatocin kasashen yammacin duniya da Bankin Duniya, da kuma zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, abinda ya tilastawa Janar al-Burhan maida Firaminista Hamdok kan mukaminsa a watan da ya gabata a karkashin wata yarjejeniya da suka kulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.