Isa ga babban shafi
Sudan

An harbe mutane 3 a Sudan yayin zanga-zangar adawa da sojoji

Jami'an tsaro sun harbe wasu masu zanga-zanga uku a Sudan tare da harba hayaki mai sa hawaye a ranar Alhamis, a daidai lokacin da jama'a suka sake yin dandazo a babban birnin kasar Khartoum da wasu biranen kasar, domin cigaba da zanga-zangar adawa da sojoji.

Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Sudan, yayin gangami a birnin Khartoum.
Masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin sojoji a Sudan, yayin gangami a birnin Khartoum. © Marwan Ali, AP
Talla

Akalla mutane 60 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon murkushe masu zanga-zangar, tun bayan juyin mulkin da dda sojoji suka yi a watan Oktoba, matakin da ya katse yunkurin kawo sauyi na demokradiyya.

Kwamitin likitocin Sudan ya ce dukkanin mutanen da aka kashe a ranar ta Alhamis sun mutu ne sakamakon harbin da jami’an tsaro suka yi a lokacin da ake gudanar da zanga-zanga a garuruwan Omdurman da Bahri, da ke gabar kogin Nilu daga birnin Khartoum.

Dubban 'yan Sudan yayin zanga-zanga a birnin Khartoum.
Dubban 'yan Sudan yayin zanga-zanga a birnin Khartoum. AP - Marwan Ali

Masu zanga-zanga a Sudan dai sun sake yin yunkurin isa fadar shugaban kasa da ke babban birnin kasar domin ci gaba da matsin lamba kan sojoji, wadanda juyin mulkin ya dakatar da shirin raba madafun iko da aka tattauna bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Sojojin kasar ta Sudan dai na kare kansu da hujjar cewa juyin mulkin da suka yi na a matsayin "gyara" da ake bukata don daidaita tsarin mika mulki, gami da nanata matsayinsu na halatta zanga-zangar lumana, tare da shan alwashin hukunta wadanda suka haddasa asarar rayuka.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Khartoum ta ce jami’an tsaro sun kai samame asibitin Arbaeen da ke Omdurman, inda suka far wa ma’aikatan lafiya tare da raunata masu zanga-zanga, zalika ta ce sojojin sun yiwa asibitin koyarwa na Khartoum kawanya tare da harba hayaki mai sa hawaye a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.