Isa ga babban shafi
Sudan

Firaministan Sudan ya yi murabus

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya yi murabus bayan sama da watanni biyu da aka yi masa juyin mulki, yayin da kuma sojoji suka yi amfani da karfi wajen murkushe masu zanga-zangar adawa da su.

 Abdallah Hamdok
Abdallah Hamdok REUTERS - HANNIBAL HANSCHKE
Talla

Tun dai shekara ta 2019, Sudan ke fuskantar cikas a yunkurinta na koma kan turbar demokuradiya bayan kifar da gwamnatin Omar al-Bashir.

Sai dai kasar ta sake rincabewa bayan Janar Abdel Fattah Al-Burhan ya jagoranci juyin mulki a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata tare da tsare Hamdok.

Kodayake sojojin su saki Hamdok a ranar 21 ga watan Nuwamba karkashin wata yarjejeiya wadda a cikinta ya amince ya shirya zaben shugaban kasa a tsakiyar shekara ta 2023.

A yayin gabatar da jawabi ga al’ummar kasar ta kafar talabijin, Hamdok ya bayyana cewa, ya yi iya kokarinsa na ganin  ya kare kasar daga tsunduma cikin bala’i.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.