Isa ga babban shafi

Likitocin Sudan sun kaddamar da zanga-zanga

Likitocin Sudan sun kaddamar da zanga-zanga a yau Lahadi, don bayyana takaicinsu kan muna-nan hare-haren da jami'an tsaro ke kaiwa ma’aikatan kiwon lafiya, yayin zanga-zangar da dubban ‘yan kasar ke yi ta adawa da mulkin sojoji.

Likitoci a wani asibiti
Likitoci a wani asibiti © Getty Images/Eric Audras
Talla

Yayin zantawa da manema labarai, daya daga cikin likitocin da suka yi zanga-zangar a yau Lahadi a birnin Khartoum, ya ce ko a baya bayan nan sai da jami’an tsaro suka harba hayaki mai sa hawaye a cikin asibitin da yake aiki.

Zanga-zangar likitoci
Zanga-zangar likitoci AFP/FAROUK BATICHE

Zanga-zangar likitocin dai dai ita ce ta baya-bayan nan a Sudan, inda a makon jiya, a wata  zanga-zangar ta daban, dubban mutane a arewacin kasar suka dates tituna, bayan da suka fusata da karin farashin wutar lantarki da aka sanar.

A ranar 25 ga watan Oktoban bara sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, suka yi wa gwamnatin rikon kwarya juyin mulki, lamarin da ya haifar da cikas ga yunkurin mika mulki ga farar hula zalla, tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019 bayan zanga-zangar da matasa suka yi.Matakin sojojin na Sudan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kasashen duniya tare da haifar da karin jerin zanga-zanga, inda ko a yau Litinin ake sa ran sake gudanar da wani gangamin Zuwa yanzu mutane 64 suka mutu yayi zanga-zangar adawa da mulkin sojojin a Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.