Isa ga babban shafi

Sojojin Sudan sun kashe akalla mutane 79 tun bayan juyin mulki

Jami'an tsaron Sudan sun kashe wani mai zanga-zanga a jiya Lahadi a yayin da suke murkushe dubban masu zanga-zangar neman mulkin farar hula, lamarin da ya kai adadin da aka kashe tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara zuwa akalla 79.

Zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan
Zanga-zanga a birnin Khartoum na kasar Sudan REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Fiye da watanni uku bayan kwace mulki a ranar 25 ga watan Oktoba karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan a kasar mai fama da rikici da ke yankin arewa maso gabashin Afirka, aka dauka ana zanga-zangar neman a maido da tsarin mulkin farar hula. Juyin mulkin, daya daga cikin wasu da dama a tarihin kasar Sudan bayan samun ‘yancin kai, ya kawo cikas ga tsarin raba madafun iko tsakanin sojoji da fararen hula da aka yi ta tattaunawa mai cike da sarkakiya bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Khartoum na kasar Sudan
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Khartoum na kasar Sudan © Marwan Ali/AP

An kuma gudanar da zanga-zangar ta Lahadi a wurare da suka hada da garuruwan Atbara da Dongola da ke arewacin kasar, da kuma yankin Darfur da ke yammacin kasar.

Zanga-zangar kiyamar sojoji a Sudan
Zanga-zangar kiyamar sojoji a Sudan - AFP

A birnin Khartoum, jami'an tsaro sun toshe wasu muhimman gadoji tare da rufe titunan da ke kan hanyar zuwa fadar shugaban kasar, kamar yadda suka sha yi a tsawon watanni ana zanga-zangar da aka saba yi.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce hukumomin kasar, a cikin 'yan makonnin nan, sun kama wasu karin mutane 45 gabanin tattakin na ranar Lahadi.

Kungiyar likitoci masu zaman kansu ta ce akalla mutane 79 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a zanga-zangar adawa da juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.