Isa ga babban shafi
Sudan

Ruftawar mahakar ma'adanai a Sudan ya kashe mutane 13

Wasu masu hakar ma’adanai a yankin kudancin Korfadan na kasar Sudan su 13 sun hallaka, bayan da kasa ta zaftare ta kuma rufto a kansu. Rahotanni sun ce da yammacin jiya ne kasar ta rufto kan masu hakar gwal din, inda kuma ta danne su baki daya, lamarin da ya yi sandiyyar mutuwar ta su.

Ruftawar mahaku na shirin zama ruwan dare a Sudan.
Ruftawar mahaku na shirin zama ruwan dare a Sudan. AFP
Talla

Bayanai na cewa kaso 80 cikin dari na albarkatun gwal da sudan ke da shi ana dibar sa ne ta barauniyar hanya.

A cewar Warsha Nasir guda daga cikin manyan kusoshin gwamnati a yankin na Kordafan ya ce an sami mutane da dama da suka jikkata a dalilin zaftarewar kasar.

A cewar sa masu hakar ma’adanan ba bisa ka’ida suke aikin su ba, don haka ne suka gaza samun daukin ma’aikatan gwamnatin don basu ceto saboda rashin zuwan labarin ga gwamnati kan lokacin da ya dace.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun zaftarewar kasa kan masu aikin hakar ma’adanai musamman wadanda ke yi ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.