Mutum daya ya mutu bayan sabunta zanga-zangar adawa da sojoji a Sudan
Jami'an tsaron Sudan sun kashe mutum guda a jiya Asabar, yayin zanga-zangar da aka sabunta ta adawa da mulkin sojojin kasar sojoji, wadanda juyin mulkin da suka yi ya kawo cikas ga shirin sake mika jagorancin kasar ga farar hula a shekarar bara.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da kwamitin likitocin sudan ya fitar, ta ce mutumin da ba a tantance ba, ya mutu ne sakamakon harbinsa da aka yi da harsashi a kirji, yayin zanga-zangar adawa da sojojin a birnin Omdurman.
Mutuwar ta baya-bayan nan dai ta sanya jumillar adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Sudan kaiwa 96, tun bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi a ranar 25 ga watan Oktoba karkashin jagorancin babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan.
Kimanin mutane 100 ne suka jikkata ranar Alhamis da ta gabata kadai, yayin zanga-zangar adawa da mulkin sojojin Sudan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu