Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci bincike kan kisan masu zanga-zanga tara a Sudan

Shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Mitchell Bachelet, ta yi kira ga mahukuntan Sudan da su kaddamar da bincike mai zaman kansa kan yadda jami'an tsaro suka kashe masu zanga-zanga akalla tara ciki har da yaro mai shekaru 15, wadanda ke cikin dubban ‘yan kasar da suka sake fita babbar zanga-zangar neman kawo karshen mulkin sojoji.

Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Khartoum babban birnin kasar Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Zanga-zangar da ta sami halartar dubun-dubatar jama'a a fadin kasar ta Sudan, ta fuskanci tashin hankali mafi muni a bana.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa masu zanga-zanagar na rike da kwaleyen da suka rubuta "Dole mu kawo karshen mulkin Al-Burhan" da kuma hotunan mutanen da aka kasha a zanga-zangar da da ‘yan kasar ke yi akai-akai tun hambarar da gwamnatin Omar Al-Bashir.

Kawo yanzu dai adadin wadanda suka mutu sakamakon tashe-tashen hankulan da suka barke yayin gudanar da zanga-zanga a Sudan ya kai mutane 113, tun bayan da sojoji suka karbe mulkin kasar a karkashin jagorancin babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan a watan Oktoban da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.