Isa ga babban shafi

Sudan: Masu zanga-zanga sun ci gaba da Allah wadai da mulkin soja

Dubban masu zanga-zangar a Sudan sun gudanar da gangami a babban birnin kasar ranar Lahadi domin neman kawo karshen mulkin soji da rikicin kabilanci da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 100.

Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Masu zanga-zangar adawa da mulkin sojoji a Khartoum babban birnin kasar Sudan. AP - Marwan Ali
Talla

Masu zanga-zangar na rera wakar kawo karshen gwamnatin Janar Abdel Fattah al-Burhan, babban hafsan sojin kasar da ya jagoranci juyin mulkin a bara wanda ya kawo sauyi ga mulkin farar hula bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Barkewar Zanga-zanga

Tun daga lokacin ne ake gudanar da zanga-zangar kusan mako-mako, duk da murkushe su da jami’an tsaro ke yi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 116, a cewar likitoci da masu rajin kare demokradiyya.

Tun bayan juyin mulkin da aka yi a bara, Sudan -- wacce ta kasance daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya -- ke fama da tabarbarewar tattalin arziki da kuma tsaro kari da rikicin kabilanci a yankunanta masu nisa.

Rikicin Kabilanci

A ranar 11 ga watan Yuli ne rikicin kabilanci ya barke a kudancin jihar Blue Nile, inda mutane akalla 105 suka mutu, wasu 291 suka samu raunuka, lamarin da ya haifar da zanga-zangar neman a yi adalci tare da yin kira da a zauna tare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.