Isa ga babban shafi

Jerin shugabannin Afrika 13 mafiya dadewa kan karagar mulkin kasashensu

A lahadi mai zuwa shugaba Paul biya na Kamaru zai cika shekaru 40 akan karagar mulki matakin da ke mayar da shi shugaba na biyu mafi dadewa akan mulkin wata kasa a kaf nahiyar Afrika bayan takwaransa Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea.

Shugaba Paul Biya na Kamaru shi ne shugaba na biyu mafi dadewa a kan karagar mulki.
Shugaba Paul Biya na Kamaru shi ne shugaba na biyu mafi dadewa a kan karagar mulki. © AFP
Talla

Shugaba na farko mafi dadewa a mulkin shi ne Teodoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea mai shekaru 80 wanda ke cika shekaru 43 akan mulki bayan fara jagorantar kasar tun daga juyin mulkin da ya yi a ranar 3 ga watan Agustan 1979, yayinda kuma ya ke shirin  neman wa’adi na 6 da zai bashi damar kara shekaru 7 nan gaba.

Shugaba na Biyu shi ne Paul Biya na Kamaru mai shekaru 89 da ke cika shekaru 40 bisa karagar mulki kana Denis Sassou Nguesso na Congo-Braziville mai shekaru 78 da ke cika shekaru 38 sannan Yoweri Museveni mai shekaru 78 da ke shafe shekaru 36 a karagar mulkin Uganda.

Akwai kuma Sarki Mswati na III da ke cika shekaru 36 kan mulki bayan da haye kujerar sarautar kasar tun yana da shekaru 18 a 1986, sannan Isaias Afwerki na Eritrea da ke jagorancin kasar tun bayan samun ‘yanci a 1993.

Sauran shugabannin da tarihi ba zai manta da su ba saboda dadewarsu a karagar mulkin kasashen Afrika, sun kunshi Sarkin sarakuna Haile Selassie na Habasha wanda ya yi mulkin shekaru 44 gabanin hambarar da shi a 1974 kana Moamer Kadhafi na Libya da ya yi mulkin shekaru 42 gabanin kisan shi a 2011 kana Omar Bongo na Gabon da ya mulki kasar shekaru 41 kafin mutuwarsa a 2009.

Akwai kuma shugaba Jose Eduard dos Santos da ya mulki Angola shekaru 38 kafin sauka a watan Satumbar 2017 sannan Robert Mugabe na Zimbabwe da ya yi mulkin shekaru 37 kafin tilasta masa sauka a 2019 kana Omar al-Bashir na Sudan da ya yi mulkin shekaru 30 tukuna Idris Deby Itno na Chadi da shima ya mulki kasar tsawon shekaru 30 gabanin mutuwarsa a fagen daga cikin watan Aprilun 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.